─✿ ME YASA KORAFIN RASHIN WARKEWA YAYI YAWA BAYAN SHAN MAGANIN SANYI ? :═✿ ★★

═─✿ ME YASA KORAFIN RASHIN WARKEWA YAYI YAWA BAYAN SHAN MAGANIN SANYI ? :═✿
  ★
•    

Sharadin Shine Ayi Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana 🔔🔔🔔

Da yawa za ka ji  macce tace tayi ta shan maganin Sanyi Amma ga banza. 

Akwai wasu abubuwa da ya kamata a kiyaye lokacin da ake shan maganin Sanyi. 

A LURA DA KYAU. 

1. Idan Namiji da Matar sa suna dauke da wannan cutar, abinda ya dace dukkansu biyu zasu fara shan magani, bawai matar kadai ba, muddin daya daga cikinsu ne yake shan magani dayan kuma baya sha to, akwai matsala.

2. Duk matar da aka dora ta  akan magani duk lokacin data cire wandon ta yakamata ta wanke shi da antiseptic, kafin ta maido wannan shina yana taimakawa wajen warkewa, koma a hakura da saka pant Gaba daya sai an Sami waraka.

3. Idan akaci gaba shan magani kuma ba'a kiyaye wasu hanyoyin da suke kawo wannan cutar ba shima akwai matsala sosai. Ma'anar haka shine dole ne a kaucewa hanyar da ka iya kawo cutar a jikin. 

Misali, dole ne ayi amfani da bayan gida mai tsabta. 

 A kiyaye wajen wanke dubura bayan an amfani da toilet. 

4. Kauracewa Jima’i lokacin da ake shan magani yana taimakawa sosai wajen samun waraka.

Idan ba a kiyaye wannan ba gaskiya yana da wahala a samu waraka yanda ake bukata.

5.  Kar ki yi amfani da pants din wata komai lafiyar ta, kuma Kar ki ba ri wata tayi amfani da na ki pants. 

6. Ga matar da ke da kishiya dole ne su sha magani a lokaci daya kuma tare da mai gidan, idan ba ayi haka, to ko zaki shanye maganin duniyar a banza. 

7. Duk wacce aka dorata akan maganin sanyi da ta fara sha toh dole ta daina shan sukari sai ta warke, da kuma duk wani nau'in abubuwa masu sukari, lemon kwalba Dana roba. Idan bazaki iyaba toh nemi zuma ko mazarqwaila.....

A karshe inna shawartarku kudinga tabbar kun kwarara ruwa sosai a bandaki idan kuka shiga yin fitsari musamman taron jama'a, sai ki samu ruwa ishashe ki wanke jikinki amma idan ki bari sanyi ya kamaki Allah Ya kyauta kawai dan wallahi kin zama sorry......

Akwae abubuwa da dama wadanda ya kamata yan mata budurwai kusani Amma sam bakwa bincike saboda bashine a gabanku sai bayan Kun kusa aure sai kudawo Kuna neman abubuwan gyaran.

A KULLUM BANDA WANI BURI A RAYUWA WANDA YAWUCE NAGA MATA  DA MAZA SUNA PARIN CIKI SOSAE INADA BURIN NAGA KUNA PARIN CIKI A GIDAN AURENKU SABODA PARIN CIKIN KU SHINE NAWA IDAN KEMA KINASON PARIN CIKIN NAWA TO KUYI SHARING DIN WANNAN RUBUTUN DOMIN YAN UWA SU AMFANA.

Allah Ya karemun da lafiya, wannan situation din da muke ciki Allah ya kawo mana dauki albarkacin fiyayyen halitta Annabinmu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Post a Comment

Previous Post Next Post