LEMON TSAMI 🍋: lemon tsami na daya daga cikin ya'yan itatuwa da jama'a sukeamfani da shi wajen yin abubuwan da dama.

LEMON TSAMI 🍋: 

lemon tsami na daya daga cikin ya'yan itatuwa da jama'a suke
amfani da shi wajen yin abubuwan da dama.

lemon tsami na da matukar muhimmanci ga dan Adam
musamman ma wajen.

🍋→ gyara fuska 
Saboda haka muka kawo
Amfani dashi domin gyaran fatar fuska.

➽ lemon tsami 🍋
➽ zuma 🍯
➽man zaitun

Ki Debi Rabin cokali ruwan lemo tsami da kuma Rabin cokali
zuma sai a kwaba su, daga nan ki shafa a fuskarki na tsawon
minti ¹5 sannan ki wanke da ruwan sanyi idan kina da fata mai
gautsi to Zaki iya hadawa da man zaitun idan kuma fatarki bata
da shi kada kisa man zaitun.

HADIN GYARAN FATA DA NONO:

wannan hadin shima yana gyara fata yana sawa fata kyau
musamman fatar fuska.

❁ nono kindirmo
❁ lemon tsami 🍋

Zaki hada Rabin cokali ruwan lemon tsami da Rabin cokali nono
sai ki kwaba sosai bayan haka sai ki shafa a fuska na tsawon minti
³0 kafin ki wanke.

Post a Comment

Previous Post Next Post