ALAMOMI DA KUMA MAGANIN KAIKAIYIN GABA.
1-Kuburin gaba
2- Caxa Launin gaba zuwa Ja.
3- Kaikayin gaba
4-Warin gaba
5-Kurajen gaba
6- Zubar da Farin ruwa a gaba.
7- Zafin Lokocin Jima'i
8- Zafin Fitsari.
YADDA MACE ZA TAKARE KANTA DAGA VAGINAL INFECTION:
(1). Kada a Tsaftace Gaba Da Sabulai masu Kashe Kwayar
Cuta : A cikin Farji akoi wassu kwayoyin bakteriya wadanda basa cutarwa kuma sunada amfani, amfaninsu shine suna taimakawa wajen bada kariya ga Farji, sai kaga wassu matan sukan wanke Farji da Sabulu ko detol haka, wadannan abubuwanda ake amfani wajen wanke farji yakan kashe bakteriya masu amfani na Farji, Sai _masu cutarwa su samu daman shiga. A kiyaye wanke Farji Da Sabulu dakuma wadansu abubuwa Wanda bamusan Kansu ba.
(2). A Tsaftace wanduna : Amfani da wandon pants, wassu matan sukan bar wandonsu yayi datti, Barin datti ko amfani pant masu datti yakan bawa kwayoyin cuta daman shiga Farji.
A Tsaftace wanduna.
(3). Wajen wanke bahaya mafi yawa mata sukan dauki kwayar cutar da take dubura zuwa Farji, wanda basa yiwa dubura illa amma sukan yiwa Farji illah.
Shawara shine afara wanke Farji kafin a wanke dubura.
(4). Amfani da pants na wassu, ta yiu wacce kuke amfani da pants daya tanada cutar Sanyi idan kinyi amfani da nata kema zaki iya dauka.
Sai a kiyaye.
(5). Mace tana iya daukan wanna cutar lokocin saduwa da namiji idan namijin yana dauke dashi, hanayar Mariya itace amfanida Condom lokocin saduwa.
(6). A kiyaye amfani da magungunan gargaji musamman wanda ake cusa su a gaba, suna taimakawa wajen samun kwayoyin cuta.
Please share.
Kuyi sharing don Allah 🙏🏿🙏🏿🙏🏿🙏🏿