MAGANIN NANKARWA Da farko dai shi Nankarwa wasu tabbai ne layilayi dasuke fitowa mace a jiki musamman wacce ke dauke daciki zuwa haihuwa Wanda idan anyi maganin sa da wuri

MAGANIN NANKARWA
 
Da farko dai shi Nankarwa wasu tabbai ne layilayi da
suke fitowa mace a jiki musamman wacce ke dauke da
ciki zuwa haihuwa Wanda idan anyi maganin sa da wuri
wato daga fitowar sa zasu iya bacewa gaba daya amma
barin shi ya dade kan hana sa bacewa gaba daye sai dai
zai dushe ya zama dan kadan kadan ake iya gani
Suna fitowa ne a wurare kamar haka :-
Cikin mace daga kasa (mara)
Cinya
Saman mama
Mazauni
Saman hannu ta wuraren hammata
Da sauran su.
 
ME KE KAWO NANKARWA ?
 
Akwai abubuwa da dama da suke sa nankarwa kamar:-
1-daukan ciki zuwa haihuwa (wannan shine babban
abinda ke kawo nankarwa)
2-ramewa tashi daya (ga mutum mai qiba)
3-yin qiba tashi guda (ga mutum mai rana)
4- gado daga mahaifiya
5-jinya na tsawon lokaci
6- damuwa mai yawa da makamantar su.
 
MATAKAN NANKARWA

Yana da matakai guda uku gasunan kamar haka:-
 
1) farko fitowar sa zaki gansu sirara yana da pink kala
sannan yakan yi kaikayi wannan matakin bashi da
wahalar magani.
 
2) zai zama ja ko ruwan bula sannan girman su zai karu
yanzun kam babu kaikayi sai lokaci zuwa lokaci zai iya
bacewa ki ya ragu ya danganta da yanayin jikin mutum.

3) zai zama fari ko ruwan silva wannan kam yana da
matukar wahalan magani sai an jure shims din sai dai ya
ragu ba wai ya bace baki daya ba.
 
HANYOYIN MAGANCE NANKARWA

Ruwa
Ruwa da Kuke gani yafi komai mahimmanci a jikin dan
Adam. Rashin shan ruwa yana sa jikin mutum ya bushe
ya tattare tare da saurin tsufa a yayin da yawan shan
ruwa kofi 8-10 kullum yake sanya taushin jiki da kyawun
fata kuma da hana wasu cututtuka da dama kama fatar
mutum da wuri.
 
MISALIN YANDA ZAKA SHA KOFI 8 ZUWA GOMA
ACIKIN KO WACCE RANA

Kofi 2 da zaran kin gama wanke baki da safe.
Kofi daya bayan karin kumallo
kofi Daya Kafin azahar kisha
kofi Daya kafin abincin rana daya bayan kin gama ci.
kofi daya da la'asar.
kofi Daya kafin abincin dare kofidaya bayan kin gama ci.
 
MAN CIKA-GIDA (CASTOR OIL)

Wannan man yana da Matukar amfani wajen
magungunan da suka shafi fata kamar maganin pimples,
cin zanzara, tabbai da sauran su.
 
YANDA AKE AMFANI DASHI
 
Ki dibi kadan sai ki sa a wuta yayi dumi sannan ki shafa a
duk inda kika san yana da nankarwa ajikin ki da dumi
duminsa ba yanda zai kona ki ba. Kiyi hakan har na
tsawon wata guda.
Ko kuma ki shafa man sannan ki dauko yadi mai taushi
na cotton ki rufe wurin dashi ki Zuba ruwan dumi a gora
ki riqa dorawa a saman yadin.
 
ALOE VERA
Ki tatse farin ruwan aloe vera kullum ki riqa shafawa a
wurin idan ya bushe sosai sai ki wanke da ruwan dumi
Ko kuma ki diba man aloe vera din chokali daya ki hada
da vitamin E oil capsule daya ki shafa a wurin.
 
FARIN KWAI
K fasa Kwai daya ki cire kwaiduwan kwan ki yar sai kiyi
amfani da fork ko whisker kiyi ta kada farin kwan har sai
yayi kauri ya yi fari tas kamar cream sannan ki shafa a
wurin nankarwan ki barshi ya bushe sannan ki wanke da
ruwan sanyi kiyi tayin hakan har na tsawon sati biyu.
 
RUWAN LEMON TSAMI
ki matse lemun tsami sai ki diba ruwan ki riqa shafawa in
circle a inda nankarwan suke har sai kinga ya bushe ki
barshi bayan minti goma ki dauraye da ruwan dumi.
Ko kuma ki hada ruwan lemun da ruwan nukakken
cucumber sannan ki shafa.
 
SUGAR
Ki hada suga da almond oil ko zaitun ko man kwakwa da
ruwan lemun tsami ki shafa tsawon minti goma sannan
ki shiga wanka.
 
RUWAN DANKALI
Ki fere dankali sai ki dauki guda daya ki dan jajjaga ki
shafa ruwan a inda nankarwan take idan ya bushe zaki
ga yayi fari sai ki wanke da ruwan dumi ki shafa zuma ko
zaitun ko man kwakwa.
 
MAN KADE
yawan shafa man kade a wurin ma yana rage shi sosai.
Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zaran sun
haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar
kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ce babu
kemikal acikin ta dan haka yana daukan lokaci kafin aga
canji kamar Sati biyu idan baki ga chanji ba sai ki dauki
wani kuma. Allah shine masani. Allah yasa mu dace
 
MAGANIN NARKARWA
1.ruwan khal farin,ki shafa a gurin for 15mins sai kiyi
wankan ki,inkin dawo kuma,sai kishafa ma gurin man
kwakwa,insha Allahu zai bace kuma skin naki zaiyi
kyau,Allahu A'Alamu.

Sirrin Rike Miji

Post a Comment

Previous Post Next Post