MAGANIN HEPATITIS B (CIWON HANTA)TAMBAYA TA 1374

MAGANIN HEPATITIS B (CIWON HANTA)

TAMBAYA TA 1374
*******************
Assalamu alaikum..,Allah ya kara taimaka muku wajen kwazo da juriya bisa ga yadda kuke taimakawa bayin Allah da fatawa da kuma magunguna.
Bayan haka ni dai na kasance mabiyin wannanzaure da dadewa,ina ganin fatawa daban daban gami da magunguna..,sai dai a iya duban da nayi malam ban ga ka tabo bangaren ciwon hanta ba (hepatitis), don hakanake rokon malam da ya taimaka mana da bayanin maganin. Allah ya sakawa malam da alkhairi. Amin
(Daga Jameel Aliyu kano)

AMSA
******
Hepatitis-B ciwo ne wanda yake kama hantar dan Adam. Kuma yana daga cikin layin Cututtuka mafiya hatsari, kuma masu saurin kisan rai idan ba'a dauki mataki ba.

Kungiyar lafiya ta duniya, da kuma Likitocin turai sunyi ittifaki akan cewa batta da magani. (Saboda ta riga ta gagaresu) sai dai akwai riga-kafin ta.

Ana daukar cutar ta duk irin hanyoyin da ake daukar cutar Kanjamau (AIDS) kamar su Jima'I, ko ta hanyar allura, ko Shayarwa, ko Qarin jini, da dai sauransu.

Amma mu a likitancin Manzon Allah (saww) a magungunan Musulunci muna da maganinta insha Allahu. Kuma su ma turawan sun tabbatar da cewa maganin namu karbabbe ne.

Kuma ga yadda abun yake:

1- Zuma tana kunshe da Sinadarai masu karfi wadanda suke da saurin Murkushe kowacce irin kwayoyin cuta acikin kankanin lokaci.

Kuma tana kunshe da wani Sinadari wanda yake taimakawa naman jikin hantar mutum ya sake tsirowa, ya maye gurbin wanda cutar Hepatitis din ta lalata.

2- HABBATUS SAUDA - tana kunshe da Sinadarai na maganin kusan dukkan cuttuttukan da zasu iya shiga jikin Dan Adam.

Sannan tana kunshe da wani Sinadari na Musamman wanda yake da tasiri wajen dawo da Qarfi da Kuzari adukkan gabobin jikin Dan Adam, tare da taimakawa wajen tsaftacewa Jinin jikin 'Dan Adam.

3 - TAFARNUWA - ita ma ANTI BIOTIC ce wacce al'ummomin duniya sukayi dubunnan Shekaru suna amfani da ita amatsayin magani.

YADDA ZAKA YI
****************
Ka samu Zuma kofi 2. Ka zuba Garin H/sauda cokali 10, garin Tafarnuwa cokali 2, garin Citta cokali 2.

Ka gaurayasu ka ajiye. Kullum da safe ka rika shan Cokali 3, idan ya rage 30 mins kafin kayi breakfast (wato karyawar safe).

Hakanan da yamma ma zaka qhrikayi. Zaka ci gaba dayi har sai lafiya ta samu.

Insha Allahu zaka samu lafiya da kuma Qarfin jiki kuma zaka warke da yardar Allah.

Wallahu a'alam.

Post a Comment

Previous Post Next Post