Ingattaccen Hadin Gyaran Nono Ga Mata Na Uwargida
Ina mata maso sun kara girman nono su yadda zai dinga bada sha'awa kuma su burgi mazajin su toh ga haddin da zasuyi.
wannan hadin yana karawa mace girman nono kuma sam ba ya faduwa. Ko da a ce tana shayarwa ne idan har tana amfani da wannan hadin sai dai mu ce Allah san barka. Uwargida, ki nemi wadannan kayayyakin:
1: Farar shinkafa
2: Garin Alkama
3: Garin habbatus sauda
4: Garin Ayaba (Plantain).
5: Gyada mai malfa (mai zabo)
6: Aya
7: Madarar gari.
8: Zuma
Za ki bare bayan plantain sai ki yayyan ka shi, ki shanya ya bushe, sai ki daka, ki hada da garin alkama da garin farar shinkafa, sai ki hada aya da gyadar ki markada sai ki tace ruwan. Bayan nan, sai ki dora kan wuta ki zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da kika hade a guri daya, sai kuma ki zuba garin madara da zuma, ki dama ya yi kauri sai ki rika sha safe da yamma.
Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati biyu kafin yaye, in kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi rigar mama, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa mamanki su tsaya sosai, ki rika sakawa. Ki yi haka na tsawon sati biyu, da yardar Allah za ki samu biyan bukata. Allah ya tamake mu.
Idan kuma baki da halin siyan duka wadannan kayayyakin da na ambata a baya to kina iya yin kunun alkama ki rika sha sau biyu a rana, amma za ki rinka sa madarar gari, wato kunun alkama da madara kenan. Ko kuma ki sami garin hulba, ki tafasa ki rika gasa nonon da shi, sai kuma ki shafa man hulban a kan nonon zaki ga abin mamaki sannan kuma zaki iya pasa kwan salwa kina shafawa a kan nonon, sai kuma ki ringa fasa guda uku kina shan su danye