AMFANIN CIYAWAR LEMON GRASS GA LAFIYA************************************************LEMON GRASS ciyawace mai kamshi sosai ana dasata a gida don kwalliya sannan ana sakata acikin shayi don kamshi wasuma suna sakata har acikin kayan girki.To ba iyanan LEMON GRASS ta tsaya ba tana taka muhimmiyar rawa afannin kiyon lafiya, wata kilama mai karatu yanada LEMON GRASS agidansa amma bansan amfaninta a fannin kiyon lafiya ba.To ga kadan daga cikin amfanint:-★ Kariya Daga Ciwon-Daji/Kansa: Shukar LEMON GRASS nada sinadari mai kamshi na “citral”, wanda binciken kimiyya ya nuna cewa yana kashe kwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba a jiki. ★Haka kuma yana inganta lafiyar kwayoyin halittar jiki gaba daya.Karin Jini Da Hana Rashin Jini: LEMON GRASS nada sinadarin “iron” mai yawa, wato sinadari maisa karin jini domin cikakkiyar lafiya da kuma hana wasu matsalolin rashin jini.★Rage Hawan Jini: Yawan sinadarin “potessium” a cikin LEMON GRASS, sinadarin mai inganta lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki, na taimakawa wajen hana hawan jini, cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki, ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar abinci da rashin haihuwa, cikin yardar Allah.★Kariya Da Hana Girman Kananan Halittu masu haddasa cututtuka a jiki da kuma hana kumburi, wuri, yayi ja, da radadin ciwo a jiki, musamman taimako ce ga masu ciwon gabbobi da sassan jiki da sauransu.Yaki da cututtukan bakteriya dana fangas: Don haka tana maganin zazzabin cizon sauro da taifot idan an yi shayi da ita, da sauransu. Haka kuma tana maganin cin ruwa na yatsun kafa da makero idan an yi amfani da manta dai da sauransu.★Maganin Mura, Zubar Hanci Da Hawaye, Kaikayin Ido, Atishawa, Toshewar HanciTace duk wani abu mai guba ga jiki: Musamman na abinci, ko wani abu mai cutarwa da fitar da su daga jiki. Tana tsaftace hanta, koda, mafitsara da sauransu.Inganta Bacci Da Kuma Yakar Rashin Bacci: LEMON GRASS nada tasiri wajen kwantar da hankali da fada da rashin bacci domin samun cikakkiyar lafiya.★Taimako Ga Masu Ciwon Suga: Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake saifa da inganta aikinta.Inganta Kwakwalwa:- LEMON GRASS na taimakawa kwakwalwa wajen maida hankali don lakantar karatu, rike karatun da kuma taimakawa wajen sarrafa karatun dama ilimi. Sinadarin “magnesium”, “phosphorus” da “folate” da ake samu a cikin ciyawar nada tasirin kyautata lafiyar kwakwalwa.★Rage Kiba: Shan LEMON GRASS musamman a shayi na narkar da kitshe. Tana sanya yin fitsari akai-akai a lokacin da take fitar da duk wani abu mai yawa da jiki baya bukata wanda zai iya

AMFANIN CIYAWAR LEMON GRASS GA LAFIYA
************************************************

LEMON GRASS ciyawace mai kamshi sosai ana dasata a gida don kwalliya sannan ana sakata acikin shayi don kamshi wasuma suna sakata har acikin kayan girki.

To ba iyanan LEMON GRASS ta tsaya ba tana taka muhimmiyar rawa afannin kiyon lafiya,  wata kilama mai karatu yanada LEMON GRASS agidansa amma bansan amfaninta a fannin kiyon lafiya ba.
To ga kadan daga cikin amfanint:-

★ Kariya Daga Ciwon-Daji/Kansa: Shukar LEMON GRASS nada sinadari mai kamshi na “citral”, wanda binciken kimiyya ya nuna cewa yana kashe kwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba a jiki. 

★Haka kuma yana inganta lafiyar kwayoyin halittar jiki gaba daya.
Karin Jini Da Hana Rashin Jini: 
LEMON GRASS nada sinadarin “iron” mai yawa, wato sinadari maisa karin jini domin cikakkiyar lafiya da kuma hana wasu matsalolin rashin jini.

★Rage Hawan Jini: Yawan sinadarin “potessium” a cikin LEMON GRASS, sinadarin mai inganta lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki, na taimakawa wajen hana hawan jini, cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki, ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar abinci da rashin haihuwa, cikin yardar Allah.

★Kariya Da Hana Girman Kananan Halittu masu haddasa cututtuka a jiki da kuma hana kumburi, wuri, yayi ja, da radadin ciwo a jiki, musamman taimako ce ga masu ciwon gabbobi da sassan jiki da sauransu.
Yaki da cututtukan bakteriya dana fangas: Don haka tana maganin zazzabin cizon sauro da taifot idan an yi shayi da ita, da sauransu. Haka kuma tana maganin cin ruwa na yatsun kafa da makero idan an yi amfani da manta dai da sauransu.

★Maganin Mura, Zubar Hanci Da Hawaye, Kaikayin Ido, Atishawa, Toshewar Hanci
Tace duk wani abu mai guba ga jiki: Musamman na abinci, ko wani abu mai cutarwa da fitar da su daga jiki. Tana tsaftace hanta, koda, mafitsara da sauransu.
Inganta Bacci Da Kuma Yakar Rashin Bacci: LEMON GRASS nada tasiri wajen kwantar da hankali da fada da rashin bacci domin samun cikakkiyar lafiya.

★Taimako Ga Masu Ciwon Suga: Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake saifa da inganta aikinta.
Inganta Kwakwalwa:- LEMON GRASS na taimakawa kwakwalwa wajen maida hankali don lakantar karatu, rike karatun da kuma taimakawa wajen sarrafa karatun dama ilimi. Sinadarin “magnesium”, “phosphorus” da “folate” da ake samu a cikin ciyawar nada tasirin kyautata lafiyar kwakwalwa.

★Rage Kiba: Shan LEMON GRASS musamman a shayi na narkar da kitshe. Tana sanya yin fitsari akai-akai a lokacin da take fitar da duk wani abu mai yawa da jiki baya bukata wanda zai iya cutar da lafiya, da dai sauransu

Post a Comment

Previous Post Next Post