vegetables soup

*VEGETABLES SOUP🥣🍲 BYgloden KITCHEN👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍲🍛🍜🍝🥣*

Abubuwan hadawa👇🏾
Man gyada
Albasa🧅
Citta 
Tafarnuwa🧄
Jajjagen attarugu da tattasai🌶️🫑
Sinadarin dandano(Maggi's)
Sinadarin kamshi
Curry
Gishiri
Nama/kifi (optional)
Kabeji🥬
Karas🥕
Broccoli🥦
Dankalin turawa(irish)🥔
Da dik wani kalan kayan ganye da kuke da su.

Da farko zaki tafasa Naman da kayan kamshi,ki ajiye gefe. Ki saka mai a wani tukunya a saka albasa,jajjagen citta da tafarnuwa,jajjagen kayan miya dik ki soya,ki saka Naman naki akai ki soya su Sai ki zuba yankakken veggies naki akai tare da yankakken irish naki,ki juye ruwan tafashen Naman tare da kara ruwa kadan(ya danganta da yanayin romon da kike buqata) ki juya su hade jikinsu Sai a rife domin su risina su kama jikinsu. Shikenan an kammala Sai ci.
Za a iya cin wannan miyar da kowane kalan girki kamar su 👉🏾Farin couscous,farar doya,farar shinkafa,farar taliya,sinasir,waina,alkubus da dai sauransu.

*✍🏾gloden 

Post a Comment

Previous Post Next Post