GAREKU MATA!!!

GAREKU MATA!!!

1... Idan Har Kika Yarda Da Cewa Namiji Ba Zai Kara Aure Ba Bayan Ya Aureki Hakika Kin Yi Rashin Hankali 'Yan Mata, Don Naga Har Alkawari Kuke Kullawa Da Samarin Ku AKan Hakan.

2... Idan Kuma Kika Ce Ba Za Ki Rike Dan Mijinki Ba (Dan Kishiya) Nan Ma Kin Tafka Shashanci Babba, Don Idan Kin Haifi Naki 'Ya'yan Babu Tabbacin Cewa Zaki Dawwama a Gidan Ko A Duniyar Ma.

3... Idan Kuwa Kika Ce Namiji Ba Dan Goyo Ba  bafa duka bane , saboda akwai wasu yan goyon Domin Kin Mance Da cewa "Ai Ke Ce Baki Iya Yanda Ake Goyon Namijin Ba.

4... Idan Kuma Kika Ce Kishiya Ba Abokiyar Zama Bace Koh Mijinki Ba Zai Qaro Wata Matar Ba Toh Ke Naki 'Ya"yan Idan Kin Haifa Jere Za Kiyi Dasu Adakin Naki?

5... Idan Kika Raina Uwar Mijin Ki, Toh Ke kuma Taki Uwar Fah? Yaya Zata Kasance Agurin Matan Yan Uwan Ki.

6... Idan Kika Azabtar Da Kannen Miji, Naki Kannen Fah? Yaya Za suyi Agurin Matan Yayyinsu?

7... Idan Kina Wulakanta Dangin Mijinki, Toh Naki Dangin Waye Zai Girmama Su?

8... Idan Kika Ce Ke Bakya Son Kishiya Toh Sauran Yan Mata Da Zawarawan Gari Suyi Yaya?

9... Idan Baki Girmama Mijinki Ba, lallai kin tafka babban kuskure saboda miji ba abin wulakantawa bane.

10... Idan Kika Ce Ke Bakya Son Kishiya Toh Kisani, Da Yiwuwar Ayi Miki Kishiyar Waje Wacce Idan Akayi Rashin Sa'a Kuma Kishiyar Nan Dai Taki Ta Waje Ta Aiko Miki Da "SAKON MUTUWA" (HIV Aids) !!

SUBHANALLAH,
Don Allah Mata A Ringa Yin
Kyakyawan Tunani.

Allah Yasa Mu Dace, Ameen!!!

©️ Nusaiba tijjani 

Post a Comment

Previous Post Next Post