Labarina Bayan Shanyewar Ɓarin Jiki

Labarina Bayan Shanyewar Ɓarin Jiki

A ranar da na sami wannan larura, na tuƙo motata tun daga Abuja har zuwa Kano cikin walwala da ƙoshin lafiya. Babu wata alama ta rashin lafiya da nake ji a jikina a lokacin. Amma saukata ke da wuya zan shiga gidana sai na ji wani matsanancin ciwon kai da hajijiya sun ɗauke ni, kafin ƙifta ido sai na yanke jiki na faɗi. Sai na yi amai, kuma ɓangarena na dama ya yi nauyi sosai har ba na iya ɗaga hannuna da ƙafata.
Amma cikin ikon Allah ina cikin hayyaci na; ina gane duk wanda ya zo kaina. Bayan makwabcina ya ji ƙaƙarin aman da na yi, sai ya rugo da gudu domin kawo min ɗauki.

Aka garzaya da ni asibiti, likita ya ce jinina ne ya hau, kuma har na sami shanyewar ɓarin jiki; ɓarina na dama ya shanye.

Abin mamaki shi ne bayan ba na iya motsa ɓarina na dama, idan an taɓa ni kuma ba na ji. Abin takaicin ma shi ne ana magana ina ji, kuma ina ganewa, amma ni ba na iya maganar. Idan ma aka tambaye ni zan gane tambayar amma bayar da amsa sai ta gagara, sai dai kawai na fashe da kuka don takaici.

Bayan an ba ni taimakon gaggawa sai aka ce za a kwantar da ni domin ina buƙatar kulawa sosai.

Bayan kwanaki biyar, muryata ta ɗan fara fitowa amma duk da haka tana sarƙewa; ba kowa ne yake ganewa ba. Sai likita ya ce jikina ya yi kyau don haka zai sallame ni. Amma zan dawo na ɗinga ganin likitan zuciya duk bayan sati biyu, sannan zan je ɓangaren "gashi".

 A lokacin da aka ce "gashi" a gaskiya na tsorata sosai saboda a tunanina zuwa za ai a riƙa saka ni cikin wani inji da yake gasa mutane da wuta.

Sai da na je likitocin ɓangaren suka yi min bayani cewa ai ni ba na buƙatar "gashi". Saboda haka, suka ce na kwantar da hankalina za a ci gaba da kula da ni har aikin ɓarin jikina ya dawo.

Haka abin yake kuwa, domin har kawo yanzu da na fara dogarawa da sanda har nake iya tafiya ba a taɓa sakamin wani abu mai zafi ko wuta a jiki na ba. Sai daga baya aka yi min bayani cewa ai likitocin fisiyo ake ce musu.

Godiya ga likitocin fisiyo domin tun ba na iya

Post a Comment

Previous Post Next Post