MAGANIN SANYI (WATO INFECTION A TURANCE)

MAGANIN SANYI (WATO INFECTION A TURANCE)

Bayani game da maganin Sanyi wato Infection da ya addabi mutane masu aure da masu shirin yin auren, musamman a wannan lokaci d muke ciki.
Masu fama da:
1. Zafin fitsari.
2. Ɗaukewar sha'awa.
3. Fitar farin Ruwa a lokacin jima'i ko kuma haka nan
4. Ƙaiƙayin gaba.
5. Fitar Quraje.
6. Ciwon mara.
7. Ƙanƙancewar gaba.
8. Fitar wani daskararren abu kama dusar awara.
9. Jin motsi a mara ko a gaban mace.
Da sauran matsalolin da ba a ambata ba waɗanda sanyi ke haifarwa.

In shaaAllah in daii an dage da yin amfani da wannan haɗin to za a samu lafiya.
Abubuwan da ake buƙata wajen haɗa wannan magani su ne kamar haka:

1. Garin Qusɗul Hindi cokali 20
2. Garin Habbatussaudā' cokali 10
3. Lemon Zaƙi
4. Lemon Tsami

Za a haɗe garukan a waje guda, sai a ɗebi cokali guda na haɗaɗɗen garin a tafasa tare da nemon Zaƙi 2 da na tsami 2 da ruwa kwanon sha guda sai a sauke a tace a riƙa shan kofi guda guda sau huɗu rana.

Idan akwai iyali to a tare za a riƙa shan maganin.

Sai dai kuma wani jan hankali ga masu irin wannan lalurar da ma sauran cututtuka.

Da yawan mutane su nayi gaugawa wajen neman sauki to kusani ba awa CUTA gaggawa.
Kuma tunda takama ka to dole kayi hakurin shan mgn na tsawon lokaci inkana son warkewa.

Danko gonbara bata kama gida dan awatsa mata ruwa ta Daina ci balbal🔥 sai hayaki , shikenan abari ace tamutu to ku za asha mamakin sake tasowar ta.

Dole asha mgn na tsawon lokaci Dan cutar itama ba ranar tazoba.

Allah yasa mu dace.

Post a Comment

Previous Post Next Post