HIKIMA KAYAN MUMINI.

-HIKIMA KAYAN MUMINI.

-Haƙuri Kala Biyu Ne: 

(1) Haƙuri Akan Abin da Kake So Amma Baka Samu Ba.

(2) Haƙuri Akan Abinda Baka So Amma Sai Ya Same Ka.

-Duk Ƙofar da Ka Ganta A Rufe Tana da Mabuɗi, Kada Ka Saki Baki Kana Jiranta ta Buɗe da Kanta.

-Duk Wanda Ya Zagi Wani Tare da Kai to Wata Rana Zai Zage ka Tare Da Wani.

-Komai A Duniya Yana da Mabuɗi, Mabuɗin ilimi Shine Tambaya, Mabuɗin Nasara Kuma Hakuri, Mabuɗin Arziƙi Tsoron Allah, Mabuɗin Zaman Lafiya Adalci da Kwatanta Gaskiya.

-Kuyi Hattara da Mabuɗai Guda Uku:

(1) Fushi, Mabudin Azaba.
(2) Tsoro, Mabudin Ƙasƙanci da Fitina.
(3) Kwadayi, Mabuɗin Wahala da Zilla.

-Baza Ka Taɓa Sauƙa A Tashar Nasara Ba Sai ka Hau Motar Haƙuri da Ƙoƙari da Sadaukarwa.

-Zuciyarka Itace Adireshinka, Harshenka Shine Ma'auninka, Gyara Harshenka Sannan Ka Kula da Ayyukanka.

-Kada Ka Damu da Masu Ƙulla Maka Sharri da Hassada, Duk Ƙoƙarinsu Basu Wuce Ƴan Sa'ido ga Abinda Allah Ya Ƙaddara Maka Ba.

-Mutane iri Uku Ne: Wasu Kamar Guba Suke, Gudunsu Ake yi, Wasu Kamar Magani Suke, Akai-Akai Ake Bukatarsu da Nemansu, Wasu Kamar Abinci Suke, A Kullum Dole ne A Nemesu, Yi Ƙoƙari Ka Zama Wanda A Kullum Ake Nemansa Saboda Amfaninsa.

-Malam! Duk Yadda Kayi Sai Wani Ya Zage Ka, Ka Manta da Mutane Kayi Komai Yadda Ya Kamata! Kuma Domin Neman Yardar Allah Ta'ala.

-Kada Ka Cuci Wanda Ya Cuce Ka, Shi Sharri Kare Ne, Ko Yayi Nisa Sai Ya Dawowa Mai shi.

-Duk Abin da Kayi Na Alkhairi Masoyanka Kawai Kake Burgewa, Su Masassada Sai Dai Su Kushe, Ko Kuma Suyi Murmushi Don su Ɓatar da Hankalinka, Amma fa Hassada ga Mai Rabo Taki Ce.

-Ka Zamo Mai Haƙuri da Bayar da Uzuri ga Wanda Yayi Maka Ba dai-dai Ba, Kada ka Damu da Mai Ƙin Ka Ko Wanda Yake
Sukar ka; Ni'ima da Rufin Asirin da Allah Yayi Maka Ne Suka  Janyo Maka.

-Kashi ka Nemi Halal Sai Ya Taimakeka, Sannan Kayi Mu'amala da Kowa Bisa Kyautatawa Tabbas Kai Ne Mai Nasara Daga Ƙarshe. 

-Waɗannan Wasu Dunƙulallun Kalmomi Ne, Wadanda Fasa Su da Fahimtarsu Sai Mai Hakima.

Bisalam ✍️💙💙❤️

Post a Comment

Previous Post Next Post