LABARI MAI CIKE DA DARASI!WANI DOCTOR NE zaune a office din shi (cikin asibiti) ya na shan A.C yana danna laptop din shi.

LABARI MAI CIKE DA DARASI!

WANI DOCTOR NE zaune a office din shi (cikin asibiti) ya na shan A.C yana danna laptop din shi.
    Kwatsam sai aka kirawo shi, cikin hanzari ya fito. Koda yazo sai ya tarar Accident ne akayi. Wani mutum ne aka kawo kwance cikin jini ko fuskar sa ba'a iya ganewa.
    Nan take doctor yayi rubuce rubuce ya miqawa wadanda suka kawo mutumin sannan ya ce musu; "Ku je ku nemo wadannan magungunan sannan ku biya kudin aikin da za ayi masa naira dubu100".
   Sai mutanen su ka ce: "Mu matafiya ne, munzo wucewa ne muka tarar da mutumin yayi hadari a motarshi shine muka taimaka muka kawo shi nan, kuma wallahi ba mu da kudin nan don Allah doctor ka taimaka".
   Cikin tsawa da fushi ya ce musu: "Lallai bazan ta6a shi ba har sai ankawo abubuwan, in kuwa ba haka ba to kubarshi ya mutu".
    Kawai sai ya ja tsaki ya fice.
AFTER_2HOURS
Sai yadawo ya duba idan ankawo abubuwan da ya ce musu, koda ya zo sai ya tarar da mutanen su na kuka sun rufe mutumin da qyalle (alamar ya mutu kenan).
   Da doctor ya ga haka, sai ya dauko wayar shi (ya na cewa bara na kira daddy naji ko ya sauka lafiya?). Koda wayar ta shiga, sai yaji qarar ringing din ya na tashi a cikin jikin mutumin da aka rufe da qyalle (mai Accident din).
   Cikin alamun mamaki Doctor ya tsinke wayar, sai ya sake kira a karo na 2 kawai sai ya sake jin sautin ringing din a jikin mutumin.
   Sai ya janye qyallen, koda ya dauko wayar a jikin gawar sai yaga ashe gawar ta mahaifinshi ce (ya samu Accident din ne kafin ya je inda ya nufa) bai gane shi bane sakamakon jinin da ya 6ata ilahirin jikinsa.

DARASI:
Yana da kyau matsalar mutane ta zama tamu, haqiqa shi taimako ba ya faduwa qasa banza ga duk wanda yayi shi, Sakayyar shi na gun Allah. Kuyi amfani da lokacin ku, dukiyar ku, qarfin ku don taimakon junan ku ko don gyaran goben ku. Allah yasa mudace duniya da lahira.

Copied.

Post a Comment

Previous Post Next Post