MAGANI 2O DA AKEYI DA GANYEN MAGARYA:

MAGANI 2O DA AKEYI DA GANYEN MAGARYA:

Sharadin Shine Ayi Sharing 🔔🔔🔔
1. Ciwon daji (cancer) a dafa garin magarya a misalin cup daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kaucewa shan wasu rukunnan magunnan bature.

2. Miki ko kuraje a kan fatar jiki ko wani sashe na gangar jiki – sai a tafasa garin magarya da ruwan khal sai a wanke mikin ko kurjin da kyau da wadannan ruwan sai a marmasa garin magarya kadan a kan mikin bayan ya wuni a haka sai a saka ruwan dumi a wanke maganin sai a sake maimaitawa Insha Allahu za a samu sauki.

3. Cutukan ciki – kama daga kumburin cikin da baya da alaka da cin wani abinci ko abinsha, zafin ciki da yawan ciwon hanjin ciki akai akai sanadin wasu kwayoyin cuta na bacteria sai a nemi ganyen magarya mai kyau a dake sai a saka ruwan dumi a tace da kyau a sha kashi daya daga cikin kashi uku na karamin cup haka za a maimaita da yamma.

4. Saurin warke ciwo Anan, idan ana fama da jinya ko a lokacin da ake farfadowa daga wata rashin lafiya wacce ta kwantar da kai a sanda kake jin jikinka ba karfi ko kaji baka son cin komai saboda baka jin dandanonsa.

To sai ka nemi garin kwallon magarya kamar karamin cokali uku sai ka sanya zuma ka kwa6a ka sha zaka rinka yin haka a kalla sau biyu a rana a cikin kankanin lokaci zaka ji karfi da kuma dadin jikinka ko kuma mafi sauki ka nemi kwallon magarya ka ringa sha A hakika suna kumshe da dimbin sinadirran vitamin C wanda yake hura garkuwar jiki (boosts immunity) fiye da wanda ke a cikin vitamin C din da muke siya a chemist din saida magani.

5. Ganyen magarya nada karfin yakar cutukan fata (skin diseases) kama daga makero da karzuwa da kurajen fata na ba gaira ko ake kallon kamar na iska ne to za a kwa6a garin sai a shafa da man kade 

a inda matsalar ta shafa indan maganin ya dauki lokaci sai a wanke da ruwan dumi ko mafi sauki a nemi sabulun magarya mai kyau bana yaudara ba a ringa amfani da shi.

7. Yana tsaftace jini – sabili da yana dauke da sinadiran saponin, alkanoide, da triterpenoid dake gyaran jinin jikin dan adam.

8. Yawan gajiya da ciwon jiki ko yaushe sai a rinka dake ganyen a danyensa a sanya a cikin ruwan dumi a tace da kyau a sha.

9. Ganyen magarya na tsaida gudawar da ta tsananta sanadiyar lalacewar ciki matsalar daga abincine ko cin karo da wata kwayar cuta ta bacteria, anan banda gudawa a sanadin ciwon tsida HIV, za a sha cokali daya karami na 5ml a koko ko ruwan zafi. 

10. Karya sihirin maye – A gargajiyance wannan maganine da aka sha jarrabawa kuma ake samun dacewa, Idan maye ya kama mutum to sai a nemo busashen ganyen magarya a hada da wani turaren wuta da ba zamu fadi sunansa a nan ba saboda wasu dalillai to sai a zo a tirarawa wanda maye ya kama a nan take mayen zai sake shi.

11- Ana karya sihiri ta amfani da ganyen magarya sai dai ilmin yanda ake amfani da ganyen magarya a karya sihiri ya sha banban.

12. Mata masu karancin sha’awar saduwa sai su ringa shan ganyen 5ml na madara a kullum.

13. Ganyen magarya na maganin damuwa da hauhawan jini saboda kunshe yake da ninki ba ninki na sinadiran potassium

14. Ganyen magarya na maganin gyambon ciki

15. Ganyen magarya na kare cutukan hanta dana koda.

16. Yana daidaita nauyin jikin mutum 

17. Garin kwallon magarya na karawa garkuwar jiki kuzari.

18. Ana gauraya garin kwallon magarya dana dabino rabin cokali sai a sanya ruwa a tafasa a sanya zuma kadan a sha dan magance yawan mantuwa da taiyi tsanani musamman a sanda za a kwanta,

19. Matan da suka haihu zasu iya hada ganyen magarya da garin bagaruwa su tafasa sai su rinka tsarki da ruwan, wannan zai taimaka sosai wajen daidaituwa da kuma sake hadewar farji, 

20. Ana tsotsar kwallon magarya damin maganin kurajen dake tsirowa akan harshe ko a cikin baki.

Allah yasa mu dace.

Post a Comment

Previous Post Next Post