● ABUBUWAN DA MASOYA BASU SO A LOKACIN HIRA ●
Da yawan masoya na ƙorafi kan masoyansu duk da cewa matsalolin na da yawa amma zan ɗan yi duba akan wasu daga ciki.
●
●
Matsalar farko ita ce, wani namijin ya tsani jira yayin da ya je zance wajen budurwarsa, wannan daɗewar tana saka masa ƙuna cikin zuciya koda kuwa ya tawo tare da farin ciki;
● wasu mazan suna kasa jurewa sai su kiran hakan da wulaƙanci.
Yana da kyau ‘yan uwana mata da su yi haƙuri, su rage yawan jinkiri a lokacin da masoyansu suka zo domin faranta musu, don wata ta san zai zo, maimakon ta shirya tun kafin ya zo a a! Sai bayan ya zo zata fara shiryawa.
Wata ma a lokacin za ta shiga wanka, sai ya gama ɓata lokacinsa idan yana da wani uzirin nasa ma sai ya haƙura ala dole tunda kin ɓata masa lokacin da ya gama lissafa abubuwan da zai yi a wannan ranar. Sai dai kawai ya danne zuciyarsa ya nuna miki hakan babu damuwa saboda yana son ki.
Ita kuwa ta yi ta washe baki babu wadda yake so sama da ke kuma ba za ki canja ba. Ki sani a duk lokacin da ya samu wadda ta fi ki iya soyayya da nuna kulawa barinki zai ya koma wurinta. Ko kuma ku yi ta samun matsala da shi saboda kina ƙona masa zuciya, koda a ce ba kya son sa akwai hanyoyin da za ki bi domin ku rabu lafiya.
A wani ɓangaren kuma wata macen takan fito zance tana taunar cingam (chewing gum), wanda maza da yawa sun tsani hakan, idan wani na son hakan, wani ba ya so, a nawa tunanin ma babu wanda zai so hakan, akan kanki ma idan kika yi tunani sosai za ki iya gane cewa matsayinki na ‘ya mace me tarbiyya wadda ta taso cikin al’adar malam Bahaushe yin hakan ba daidai ba ne.
Wani namijin daga wannan halin da ta nuna masa zai ji soyayyarta ta fita a ransa koda kuwa akwai sauran son da yake mata, yakan kasa sanin yadda zai fito ya faɗa mata matsalarta wanda ita a nata tunanin daidai ne.