CIWON SANYI A JIKIN MACE:๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

CIWON SANYI A JIKIN MACE:

๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

Allah Ya halicci ko wacce mace da daษ—inta da kuma ni’imarta. Sai dai ace wata tafi wata, amma in har lafiyansa kalau to in namiji yayi amfani da shi zai samu biyan bukatarsa. Amma cututtukan al’aura ne suke mutukar lalata jikin ฦดa mace. Sai mace ta ษ—auka ita ce ba tada daษ—i yasa mijin baya jin dadinta. Idan har jikin mace babu ko wane ciwo na al’aura to abubuwa kaฤan zata ci ko ta sha sai ni’ima ya sakko mata mijinta ya gamsu da ita mutuฦ™a.

Ciwon sanyi wani abu ne da ya zama game duniya a duniyar matan yanzu. A cikin kashi 100% na mata 5% ne kawai basu da shi. Wannan kuwa ya haษ—a da matan aure da ฦดan mata. A rubutu da yawa mata suna bayanin illolinsa da kuma haษ—arinsa ga rayuwar mace. Idan ke budurwa ce to in kika bar shi har kika yi aure zai iya hana ki jin daษ—in aure gaba daya. Zaki dauฦ™i shekara da shekaru baki san menene daษ—in saduwa ba. Kuma zai iya cire miki sha’awa kwata-kwata. Haka nan zaki yaษ—a wa mijinki da kishiyoyinki in kina da su wanda in suka samu yin maganinku tare zai wahala, musamman maza da basa son shan magani. Kin ga sai ki yi ta wahala kina kashe kuษ—i yana dawowa saboda na waษ—ancan bai mutu ba.

Idan ke matar aure ce zai cire miki dukkan daษ—in jikin ฦดa mace. Kuma ko kin yi maganin matan miliyan ba zaki kai daษ—in wacce ba ta da infection ba in ma yayi aikin kenan. Zaki yi ta asaran kuษ—i amma wallahi ba zaki yi daษ—i ba. In ya fara shahara zai rinฦ™a sanya ษ“arin ciki, daga nan kuma ya hana ki ษ—aukan ciki gaba ษ—aya. Mijinki zai iya tsanarki ko jin haushin ki saboda infection ya cire miki dukkan ni’imar jikin mace.

Kaษ—an daga cikin alamominsa:

1.Fitan ruwa, wanda zai iya zuwa kamar ruwa amma yellow ko green tsinkakke. Ko kuma ya fito a fari ko in ce milk mai kauri sosai.

2.Wanda wannan ruwan zai haddasa miki ฦ™aiฦ™ayi a al’aurarki har ma da jikinki wani. Ki yi ta susa har wurin yayi ja. Haka nan in ya fara shahara sai ruwan ya fara wari mai tada hankali.

3.Daga nan sai ya feso miki da kuraje masu azabar ฦ™aiฦ™ayi. Wanda in ya tsarga in baki wasa ba ko a cikin jama’a ne sai kin sosa.

4.Ciwon mara da baya, wani ma yana sanya ciwon kai, jin amai, ko yin laulayi kamar mai ciki.

5.Dashewar gaba ki ji kamar kin ฦ™one, haka nan zaki ji kamar ana tsungulinki a cikin al’aurarki da wajensa.

6.Bushewar gaba koda ke budurwa ce zaki jiki a bushe a bushe. Matar aure kuma saukar ni’ima sai ya rinka mata wahala koda ta sha abun ni’imar.

7.ฦŠaukewar sha’awa gaba ษ—aya ko kiji kina yi kaษ—an kaษ—an. Kuma duk wani abun da zaki ci da ya kamata ya saukar miki da ni’ima zaki ga ke baki ganin komai.

8.Jin kamar tana ko tsutsa yana miki yawo a mararki ko ki ji motsinsa a gabanki.

9.Fashewar kafa, ki ga kullum ฦ™afarki akwai faso ko kauje wani infection ne ke sakawa.

10.Rikicewar al’ada koma rashin zuwansa gaba ษ—aya ko sanya miki ciwon ciki. Ga mutuฦ™ar buษ—e mace ga budurwa ko matar aure, zaki yi ta neman maganin tightening amma ko kin yi zaki buษ—e saboda infection. Dama wasu da babu adadi ko wacce da kalar nata.

11. Kumburewar gaba. Da wasu abubuwa da zai iya samunki. Wannan ya danganta da yanayin jikinki ko yanayin yanda ya dade yake ta shahara.

Kada wai ki ji kunya ki ษ“oye don kina da shi in ma ke matar aure ce ko budurwa, domin wannan halin mata ne. Mata da yawa na da shi to menene zai sa ke ki boye cuta? Yawanci maganin asibiti sumar dasu yake yi ko in ce baya kashe su duka in ba kin yi mugun nacewa bane. Haka nan koda ya warke in baki bi ka’idoji ba still zai dawo. Saboda mafiya yawan mu zamu warke amma ba zamu yi wa kan mu fada ba, sai mu koma akan wannan bad habit din. To kullum kuwa kudin ki zai kare wurin amsan maganin infection. Wani ma ya cuce ki ya baki fake, wata kuma gaba daya ta cinye kudin taki turo miki da kayan. Allah Ya warkar da masu fama da shi ya basu lafiya.

๐Ÿ’ŠKASHE INFECTION DA KAN KI๐Ÿ’Š

๐Ÿ’Š๐Ÿ’‰Waษ—annan itatuwan amfani da su yana warkar da zubar ruwan infection da ma kashe infection ษ—in baki ษ—aya, infection cuta ne wanda a ke saurin ษ—auka da kuma saurin rabuwa da shi in mutum ya san itatuwan da suke da properties da su ke kashe infection, kuma ya cire ฦ™iwiya ya rungume su. In ki ka yi haka infection sai dai ki ji labarinsa a maฦ™ota, Sadeeya tana son ki gyara, tana son ki zama gangariya, sai kin kashe infection za ki rabu da buษ—ewa, sai kin kashe infection mijin ki zai samu abun da ya kamata a ce yana samu daga gare ki my sister. Duk abun da na faษ—i ana samu a kasuwa ki nema ki fita a jirgin ban sani ba a ina zan samu.

๐Ÿ’Š1. Shan yoghurt wanda ba yi da sugar a cikinsa mai dauke da Lactic acid a ingredient ษ—in sa, ki sha kuma in za ki kwanta ki ษ—iba ki sanya a cikin al’aurarki ki kwana da shi yana kashe infection ta ciki da waje da tsayar da zubar ruwa.

๐Ÿ’Š2. Hulba yana mutuฦ™ar kashe infection da hana zuban ruwa, shan sa a ruwan zafi da zuma, ko ษ—iban garin a haษ—iye da ruwa ko yoghurt yana mutuฦ™ar kashe infection. Haka a jiฦ™a da ruwa na minti talatin ko a dafa a rinka tsarki ko zama da shi sau biyu a rana yana kashe infection na gaske.

๐Ÿ’Š3. Tafarnuwa shugaba kuma ษ—aya daga cikin manya manyan maganin infection, in kina kayan infection kuma baki amfani da tafarnuwa za ki ci wuyan gaske. Ki rinฦ™a haษ—iyan tafarnuwa ko da kwaya ษ—aya ne idan kin tashi da safe, ko ki rinฦ™a haษ—iya tare da yoghurt ษ—in da na yi bayani a farko. Idan wurin ya ishe ki da ฦ™aiฦ™ayi da ษ—ashewa ki ษ—an daka ki yi mixing da coconut oil ko zaitun ki shafa idan abun da ki ke ji ya tafi ki dakatar. Za ki iya shan Man tafarnuwa da shafa shi a ฦ™asan ki domin kashe infection, ki rinฦ™a yin zallan miyansa da ษ—an tarugu kina ci a abinci in ba za ki iya amfani da ษ—anye ba.

๐Ÿ’Š4. Apple Cider Vinegar wato ruwan khal yana kashe infection da tightening gaban mace, a dafa ruwa a surka a zuba kamar cokali biyu babba a zauna a ciki na minti 10, ko a rinฦ™a kama ruwa sau biyu ko uku a rana, sannan a rinฦ™a shan sa a ruwan zafi ko lipton.

๐Ÿ’Š5. Ganyen raihan wato basil yana tsayar da zuban ruwa da ma kashe infection, idan babu ษ—anyen sai garin a kwaษ“a da zuma ko madara ana shan babban cokali sau biyu a rana infection zai tafi.

๐Ÿ’Š6. Ganyen gwaiba maganin infection ne, ki dafa shi ki na sha sau uku a rana zai tsayar da zuban ruwa ya kuma kashe infection.

๐Ÿ’Š7. Ganyen rumman yana warkar da infection da tsayar da zuban ruwa mai wari da ฦ™arni, in an samu fruit din a sha, in ba a samu ba a nemi ganyen a sha da ruwa ko madara kullum da safe kafin breakfast.

๐Ÿ’Š8. Cin ayaba biyu kullum da safe zai taimaka wajen tsayar da ruwan infection, za ki iya niฦ™a shi tare da zuma cokali biyu ki sha zai yi har da maganin mata.

๐Ÿ’Š9. Neem wato dalbejiya maganin infection ne na haฦ™iฦ™a, ki yi garin sa ki sha tea spoon safe da yamma a cikin madara, ko kuma ki daka danyen sa ki dafa da ruwa na minti goma in ya huce ki rinฦ™a kama ruwa da shi safe da yamma har sai kin daina jin ฦ™aiฦ™ayi kuma zuban ruwan ya tsaya. Haka nan in akwai ฦ™uraje sosai ki jajjaga ki zuba coconut oil ko zaitun in babu ki ษ—ebi zallan sa ki shafa a dukkanin wurin da kuraje suka feso na minti 30 sai ki wanke. Ki siyo oil ษ—in ki rinฦ™a shafawa a gabanki in da ki ke jin ciwo da ฦ™aiฦ™ayi, haka nan za ki iya shan tea spoon na man safe da yamma.

๐Ÿ’Š10. Turmeric wato kurkum yana kashe infection, ki rinฦ™a cin sa a abinci ko ki samu madara ki dan dafa kadan ki zuba tea spoon na shi ki sha rabin kofi safe da yamma zai mutu, zai hana wannan zuban ruwan mai wari.

๐Ÿ’Š11. Aswakin mata ko Aswakin zaki yana kashe infection da tsayar da discharge, ki dafa shi har sai ruwan ya canza kala ki sha rabin kofi safe da yamma, ko rinka shan tea spoon na garin safe da yamma da madara.

๐Ÿ’Š12. Man kwakwa mai kyau pure one yana kashe infection da hana duk wani matsala a ฦ™asan ki, ki rinka samun auduga kina goge wurin da shi safe da yamma kuma ki ษ—an sa a ciki zai kashe infection ya rage zuban ruwa.

๐Ÿ’Š13. Malmoh maganin infection ne, yana wanko duk wani ruwan da infection ke fitarwa a jiki, yana kuma gyara vaginan mace, ki dafa shi ki sha kuma ki rinฦ™a kama ruwa ko zama a ciki.

๐Ÿ’Š14. Green tea yana kashe infection na haฦ™iฦ™a da cutuka masu yawa, ki siyo green tea ki rinka shansa ko da zafi ko da sanyi duk ba damuwa, ka da ki saka sugar sai zuma.

๐Ÿ’Š15. Tazargade maganin infection ne na haฦ™iฦ™a, yana kashe infection, tsayar da zuban ruwa da duk wani matsalar da suka shafi ฦ™asan ki, ki tafasa kina sha safe da yamma har sai ciwon ya tafi.

๐Ÿ’Š16. Aloe vera maganin infection ne sosai, domin kashe infection da tsayar da discharge a cire abun cikin a ษ—an jajjaga a zuba ruwa ana shan kofi ษ—aya da safe da yamma, kuma a rinka inserting gel din a cikin al’aura zai kashe kuraje, hana ฦ™aiฦ™ayi, ษ—ashewa da budewa.

๐Ÿ’Š17. Babunaj da hulba suna kashe infection a dafa kaษ—an a zuba zuma a sha zai kashe infection.

๐Ÿ’Š18. Bagaruwan mata yana kashe infection a dafa shi tare da tafarnuwa da kanunfari a zauna ciki ko a kama ruwa zai kashe shi ya gyara ฦ™amshin wurin.

๐Ÿ’Š19. Alum yana kashe infection, a dafa ษ—an ษ“angale ana kama ruwa da shi yana rage buษ—ewa da kashe ฦ™uraje, ฦ™aiฦ™ayi da ษ—ashewa.

๐Ÿ’Š20. Lalle yana kashe infection sosai, rage budewa da wari. A dafa shi tare da kanunfari a zuba musk, tafarnuwa, da bagaruwan mata ana zama a ciki ko tsarki.

๐Ÿ’Š21. A samo ganyen Magarya a dafa da lalle a na zama ko tsarki infection zai mutu ko ya ragu.

๐Ÿ’Š22. Shammar fennel kenan yana kashe infection in ana shan tea sa ko a daka a sha da madara.

๐Ÿ’‰๐Ÿ’ŠSai koyon tsafta, gyara, da canza way of life ษ—inki, in zaki shekara amfani da maganin infection muddin baki daina abubuwan da suke ฦ™aro bacterian ba za ki rabu da su ba. Allah Ya sa mu dace.

๐Ÿ’Š๐Ÿ’‰Ban san adadin magungunan infection waษ—anda ki ke da su a cikin gidan ki ba, bana son ki da kashe kuษ—i mace ta gari, bana son ki da wari, ฦ™arni da zuma ruwa, ki shigo jirgina mu haษ—u mu kashe infection ya tafi ya bar jikin mata baki ฤaya.


Post a Comment

Previous Post Next Post