SIRRIN MA'AURATA BABIN FARKOgyaran hakora.

SIRRIN MA'AURATA 
BABIN FARKO

gyaran hakora.
tabbas yana daya daga cikin burin 'ya mace musamman 'yar kwalisa wato ace tana da fararen hakora,sau da dama rashin kula dayin brush akai akai shine yake jawowa aga hakoran mutum sunyi yellow.
To amma idan har kina kula dasu yar uwa to ba abinda zai sa hakoranki su canza launi daga farare zuwa wata kalan daban ga kadan daga cikin abinda yake lalata mana hakora: -yawan shan kayan zaki da suka hada da sweet,chocolate dss -rashin yin brush bayan shan drinks mai kala misali kamar zobo -rashin wanke baki bayan cin abinci Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da suke jawo dakushewan hakori amma yar uwa zaki iya bin hanya mafi sauki wajen magance hakan. 
idan har hakoranki sun kasance ba farare ki ringa amfani da 
-lemon tsami yar uwa yadda zakiyi zaki yanka lemon tsami ki matse ruwan sai ki kuskure bakinki dashi zaki iya amfani da hannunki ko brush wajen cuccuda hakoran 
-amfani da aswak domin yana taka muhimmiyar rawa wajen sa hasken hakora 
-ga wanda bashida wadatar maclean zai iya amfani da gawayi ya dakashi sai ya dansa gishiri kadan ya wanke bakin 
-kuskure baki da ruwa bayan cin abinci ko abin sha 
-inda hali yin brush akalla sau 2 zuwa 3 a rana 
-Yin brush kafin kwanciya bacci Ina fatan wadannan abubuwa dana lissafo zasu taimaka wajen gyaran hakoranmu. 

Yar yola✍️📖

Post a Comment

Previous Post Next Post