CUTUTTUKA GOMA DA GANYEN MANGURO KE MAGANI.
1-Maganin ciwon suga.Ganyen manguro na kumshe da sinadirin tannis da kuma anthocyanins mai taimakawa matuka dan warkarda ciwon suga.
...idan dai likitoci sun baka tabbacin cewa kana da ciwon suga ko ya kasance ciwon na addabarka to ga maganin da zaka jarraba.
Kasashen Turawa musamman wadanda suka ci gaba da kuma kasar India sun kasance masu amfani da ganyen manguro dan warkarda ciwon suga.
...za a nemi ganye 4 zuwa 5 sai a dan sa6e haka ta yanda za aji dadin tafasa shi.Sai a sanya ruwa babban cup a tafasa a tace a ajiye sai da safe washe gari a sha cup daya madaidaici kamin a karya.
2.Ganyen manguro na maganin hauwauwar jini.
...anan za a nemi ganyen manguro sabon tofo sai a sa6e a tafasa a fake shan rabin cup da safe, rabi da yamma.
..3 ..ganyen manguro na warkarda basir: sai a nemi ganyen mai dan yawa haka a shanya a cikin rana idan ya bushe sai a dake a zanka sanya cokali daya a cikin ruwan dumi rabin karamin cup sai a tarfa zuma a sha.
..4 ..ganyen manguro na maganin cutukkan baki kamar kuraje ga harshe, ko kuraje a cikin baki masu radadi, ko zubar jini daga hakora, da makamantansu.
...sai a tafasa ganyen a fake sha safe da yamma haka zalika za a rinka sanya gishiri dan kadan haka a cikin ruwan a sanda aka tafasa su sai a zan wanke baki dasu a kalla sau uku ga wuni.
.5 ..ganyen manguro na maganin kunar wuta. .sai a nemi ganyen a shanya har sai ya bushe a kone ya koma toka sai a zanka marmasawa ga inda kunar take dukda yake akoi zafi.
6.Ganyen manguro na maganin cutukan ciki.
.7 ..ganyen manguro na huce zafin jiki da rashin hutu ko natsuwa (stress and anxiety) .sai a tafasa ganyen manguro a sha ayo wanka.
.8.Ganyen manguro na maganin cutukan huhu kamar tari, mura, sanyin kitji da sauransu.
9.Ganyen manguro na inganta lafiyar mahaifa da kuma samun damar haihuwa.
.10 ..ganyen manguro na maganin makakin makogwaro da ciwon wuya ko kurajen da ka iya fitowa a cikin makogwaro (throat infections) .