BASA ZUWAN KAI(Releasing)prt-2

DALILAN DAKE SAWA WASU MATAN BASA  ZUWAN KAI(Releasing)

prt-2

3: Auren Dole- Da yake shi Jima'i ana yinsa ne da kwakwaluwa amma bada zuciya ba, wannan yasa duk mutumin da bai samu natsuwa ba bazai taba gamsuwa a Jima'ince ba.
Matan da aka aura musu mazan da basa so yana da wuya suyi zuwan kai. Bama zuwan kan ba hatta dadin Jima'i ma ba zasu ji ba.
Don haka muddin tana tare da wannan mijin har tsawon lokaci haka zata yi ta zama ba tare da yin zuwan kai ba a Jima'i.
Don haka duk yadda mace take da wani damuwa a ranta to babu yadda za ayi ta iya yin zuwan kai har sai ta ajiye wannan damuwar a gefe tukun.

4: Tsayawar Al'ada: Matan da suka daina yin al'ada koda a baya suna zuwan kai to fa suna iya daina yi a lokacin da suka daina al'ada.
Wani hikiman da Allah SWT Ya kimtsa game da al'adar mace shine, yakan sata yin sha'awa kamin ta soma, tana yi da bayan ta yi wanka, hakan ne yakan sata son kusantar namiji, daga kusantar ne kuma ciki yake shiga sai a samu haihuwa. Don haka a lokacin da mace ta daina al'ada sha'awanta game da son Jima'i yana raguwa. Idan ma tayi bata jin dadin sa kamar yadda take ji a baya, rashin jin wannan dadin kuma shi yake hana ta zuwan kai.
Shi yasa masana suka tabbatar da cewa da zaran mace ta daina al'ada to yana da wuya tayi zuwan kai duk da yanzu akwai magungunan da tsoffin matan suke amfani dasu domin samun gamsuwa.

5: Matsalolin Rashin Lafiya- Akwai wasu cutukan da suke hana mata yin zuwan kai a cewar masana. 
Cutaka na ciwon zuciya dana sugar duk suna iya hana mace yin zuwan kai. 
Haka nan wasu kwayoyin magungunan da mace take amfani dasu suma suna iya hanata zuwan kai. 

Wadannan sune manyan abubuwan da suke hana wasu matan yin zuwan kai.
Sai dai shi rashin zuwan kan mace baya hana ta jin dadin Jima'i. 
Zuwan kan nata shike sata kara son mijin da take aure. Don mace bata zuwan kai hakan ba wai yana nufin baza ta ji dadin Jima'i bane, sai da wannan kololuwar jin dadin da hakan ke samarwa baza ta samu ba.
✍️
Tsangayarmalam
Via Ustaz Usman

Post a Comment

Previous Post Next Post