fried peppers chips

SPECIAL FRIED PEPPER CHIPS🌶🍠😋

ABUBUWAN BUQATA👇
Irish🍠
Attaruhu da tattasai 🌶
Man gyada
Sinadarin dandano 
Sinadarin kamshi
Curry
Albasa

YANDA ZA A SARRAFA SU👇

zaki fere irish naki ki wanke, ki yanka shi a tsaitsaye(zaki iya raba shi 4 ko 6 idan  irish din masu girma ne). Ki tsane shi a kwando ki sanya masa gishiri ki soya a ajiye gefe daya. 
A tsaftace attaruhu, tattasai, albasa a nika su kamar jajjage. Ki dora yar tukunya da mai a wuta ki sanya albasa saboda man gyadan ya dan soyu kadan, ki juye kayan jajjagen aciki ki soya ki saka sinadarin dandano,sinadarin kamshi da curry ki juya su hade jikinsu su soyu sai a dauko wancan soyayyen irish da kika ajiye a gefe ki juye shi cikin wannan sauce din ki juya su har su hade jikinsu sai ki rage wutan gabadaya ko ma ki kashe ya dan tirara jikinshi, sai a sauke. 
Shiekanan kin kammala FRIED PEPPER CHIPS. 

WANNAN HADIN YANA DADIN CI NE MUSAMMAN LOKACIN BREAKFAST KO KUMA IDAN KUNYI AZUMIN LITININ DA ALHAMIS.

BARKA DA SAFIYA!

Written by Admins of FILIN GIRKE GIRKE/MU KOYI GIRKI ZALLAH/Gloden KITCHEN

Post a Comment

Previous Post Next Post