miyar nikakken name

🍋🍋MATA MASU AJI🍋🍋

    🍋🍋MIYAR NIKAKKEN NAMA🍋🍋

Nama
Tumatir, albasa, attarugu
Mangyada, Maggi, Curry
Tafarnuwa,citta
   
     Da farko dai za'a samu Jan nama wanda bbu kitse acikinsa, sannan sai a nika a na'urar nika nama Sai a ajiyea gefe. Bayan haka sai a yayyanka albasa da Tumatir sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa.
     Bayan haka,sai a dora tukunya a zuba manyan kadan sannan a zuba albasa da tumatir da garin citta kadan da kuma jajjagen tarugu da tafarnuwa ayita soyawa sannan a dauko nikakken nama a zuba a cigaba da gauraya wa, sannan a zuba Maggi da Curry ayita gaurayawa. 
    Sai a rage wuta sannan a rufe na tsawon mintuna biyu sannan sai a sake budewa a juya harsai ta nuna sannan a sauke... 
     Za'a iya cinshi da farar shinkafa ko doya..

  

Post a Comment

Previous Post Next Post