Mace in har ta rike mutuncin kan ta.Mace in har ta rike tarbiyyar da iyayen ta suka bata.

Mace in har ta rike mutuncin kan ta.
Mace in har ta rike tarbiyyar da iyayen ta suka bata.
Mace idan har ta kula da kanta.
Mace idan har bata shigar bayyana tsaraicin ta.
Mace idan har bata yawon bariki.
Mace idan har bata sa kwadayin abin duniya ba.
Mace idan har bata kula mazan banza.
.
Wannan macen kwarjini gare ta,kuma macen kirki ce macen da kowa ne Namijin ke burin samun irin ta.

Macen da maza suke ganin kimar ta da son mallakan ta, saboda kalilan ne za'a samu.
Wannan macen namiji baya raina ta ko mayar da ita shara saboda mace ce mai daraja,Abu ne mai kima.

Takan daga darajar ta duk koma inda ta shiga sai anga kimarta.

Amma.
Macen da kike wulakanta kanki,kika mayar da kanki marar wannan kimar to kowane namiji raina ki zaiyi,kowane Namiji kallon shara zai miki.

©️ Nusaiba

Post a Comment

Previous Post Next Post