FRUITS SALAD BY Gloden KITCHEN👨🏾‍🍳

FRUITS SALAD BY Gloden KITCHEN👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳

Abubuwan buqata sun hada da kowane kalan Yayan itace da mutum yake da su,bai Zama dole sai abubuwanda aka lissafa ne za a Yi amfani da su gurin yin fruits salad ba,idan fruits guda2 kuke da shi za a iya amfani da su kuma yayi dadi...
Kankana
Abarba
Mangoro
Lemon zaki
Tuffa (Apple)
Gwanda
Ayaba 
Kankarar ruwa (ice block)
Madarar ruwa ta gwangwani
Gyada
Kwakwa (coconut)

Da farko za a fere kankana, a cire dik yayanda ke cikinta a yanka gutsi-gutsi a ajiye gefe daya,a yanka lemon zaki a cire dik yayanda ke cikinsa a yanka gutsi-gutsi a ajiye gefe daya,a yanka gwanda,mangoro,ayaba,kwakwa,Apple a yanka gutsi-gutsi a zuba a mazubi daya tare da wancan kankanar da lemon,a gyada soyayyiyar gyada a fece ta tas a zuba akai,a zuba madarar ruwa (adadin da ake buqata) a fasa kankarar ruwa akai a juyasu ,Shikenan an kammala wannan #FRUITSSALAD din na Musamman sai Sha.
Ana yin wannan lokacin shan ruwa (iftar), ko kuma bayan lunch ko kafin kwanciya,domin anso mutane su ci/Sha Abu marar nauyi kafin kwanciya bacci domin lafiyar mu...

✍🏾 Gloden  kitchen

Post a Comment

Previous Post Next Post