pepper meat

*PEPPER MEAT BY Gloden KITCHEN👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍜🍝🥣🍛🍲*

Abubuwan hadawa👇🏾
Tsokar nama🥩
Jajjagen attarugu,tattasai da albasa
Sinadarin dandano
Sinadarin kamshi
Curry
Thyme
Albasa
Zaki zuba Nama bayan kin wanke,ki zuba a tukunya ki saka sinadarin dandano(Maggi),jajjagen citta da tafarnuwa,thyme,curry,albasa da ruwa daidai Wanda zai dafa maki Naman. Ki dora kan wuta ki dafa sosai,sai ki kwashe ki soya a ruwan mai,ki juye mai a wani gurin ya kasance ya rage kadan a tukunya,ki saka wadatacciyar albasa,jajjagen attarugu da tattasai,sinadarin dandano,curry, a soya Sai a juye soyayyen Naman akai a juya su su hade jikinsu sosai Sai a saka yan an ruwa kadan kamar cokali5 a juya a rife domin su kama jikinsu Shikenan an kammala Sai ci....

Post a Comment

Previous Post Next Post