Ciwon Baya Bayan Tiyatar Ciro Jariri Ne Matsalarki?
"Caesarian Section" ko kuma "CS" a turance, tiyata ce da ake yi domin ciro jariri daga cikin uwa kai tsaye saɓanin haihuwa ta gaba. Hakan na faruwa idan aka samu tangarɗar naƙuda ko kuma bisa zaɓi.
Sai dai, ciwon baya bayan tiyatar na daga cikin ƙorafe-ƙorafen da ke biyo baya.
Daga cikin dalilan ciwon bayan na da alaƙa da yanka tsokokin bangon ciki, waɗanda rukunin tsokoki ne da suke tallafa wa gadon baya ya zauna lafiya.
Saboda haka, bayan tiyatar, tsokokin suna samun rauni, don haka tsarin taimakekeniya tsakanin tsokokin gadon baya da tsokokin bangon ciki zai samu tasgaro.
Bincike ya nuna cewa matan da aka yi wa tiyatar ciro jariri kuma suka samu kulawar likitan fisiyo bayan tiyatar sun fi samun raguwar ciwon baya a kan waɗanda ba su samu kulawar likitan fisiyo ba.
Likitan fisiyo na taka muhimmiyar rawa bayan tiyatar ciro jariri ta hanyoyin ƙarfafa tsokokin bangon ciki, magance ciwon baya, ciwon ƙugu, koyar da lafiyayyun hanyoyin riƙe jariri, ɗaga jariri, goya jariri domin kiyaye buɗewar tiyatar da kuma sauƙaƙa ko kiyaye ciwon ba.
Idan kina fama da ciwon baya bayan tiyatar ciro jariri, tuntuɓi likitan fisiyo a yau domin fara bankwana da ciwon baya ba tare da dogaro da shan maganin rage ciwo kullum ba.