YADDA ZA A TSAFTACE HAMMATA Idan an gyara jiki kada a manta cewa akwai inda ya fi muhimmanci da a kula da shi. Musamman ma bayan an aske gashin gurin, akwai hanyoyi da za a bi don hana wajen yin baki. Ababe da dama ne suke kawo hammata ta yi baki koda an aske gashin gurin. Yawan zufa da amfani da man cire gashi gashin hammata da yawan kiba da kuma amfani da turare masu karfi a hammata.

YADDA ZA A TSAFTACE HAMMATA

 Idan an gyara jiki kada a manta cewa akwai inda ya fi muhimmanci da a kula da shi. Musamman ma bayan an aske gashin gurin, akwai hanyoyi da za a bi don hana wajen yin baki. Ababe da dama ne suke kawo hammata ta yi baki koda an aske gashin gurin. Yawan zufa da amfani da man cire gashi gashin hammata da yawan kiba da kuma amfani da turare masu karfi a hammata.

GA HANYOYIN KAMAR HAKA

*AMFANI DA MAN KWA-KWA:
Babban abin da ake amfani da shi a wajen hada man zamani shi ne man kwa-kwa domin yana dauke ne da sinadarin kara haske kuma yana da vitamin E. 
A shafa man kwa-kwa a hammata a kullum a yi minti goma kafin a yi wanka. Bayan an yi haka, sai a wanke da sabulu mara karfi (wanda sinadaran da akan hada shi ba mai zafi ba ne) da ruwan dumi.

*AMFANI DA GURJI DA LEMON TSAMI:
Kamar yadda aka sani cewa ruwan lemon tsami na dada hasken fata, haka kuma gurji shi ma na dauke da sinadarin kara wa fata haske da kuma sanya ta laushi da sulbi. A hada ruwan lemon tsami da markadaddiyar gurji a guri daya sannan a shafa a hammata. A bari ya jima na tsawon mintuna goma sannan a wanke da ruwan dumi.
GARIN KURKUM DA KWAI: 

Kurkum ma na dada wa fata haske, za a iya kwaba garin garin kurkum da ruwan kwai sannan a shafa a hammata bayan mintuna goma zuwa sha biyar sai a wanke da ruwan dumi. A kullum kafin a yi wanka. 
Aski; a daina barin hammata da gashi a yi kokarin aske shi a lokacin da ya fito. Domin idan da akwai gashi a hammata, zai hana gumi bushewa zai fara tara shi yayi ta ba da wani irin wari. Sai a ga koda an fesa turare, sai a ji kamshin turaren daban, warin hammata kuma daban.
Yin amfani da wadannan ababen wajen gyaran hammata zai rage warin jiki da kuma hana fesowar kuraje da fitowar bakar kala a karkashin hammata da kuma rage gumin hammata.

Post a Comment

Previous Post Next Post