Ta fahimci mijinta aure yake son ƙarawa. Sai ta haɗa masa abinci, ta sanya Ƙwai guda 4 amma ta shafawa ko wanne kala daban, Ta kira shi ta ce, bisimillah.
Ya ce, me yasa ko wanne launinsa daban,l?
Ta ce, ka Ci, sai ka gayan bambancin. Bayan ya kammala sai ya ce, ni ban ji wani bambanci ba, duk ɗaya ne.
Ta ce, haka duk mata haka suke, ɗanɗanonsu ɗaya ne, kawai launi ne yake bambantasu.
Ya ce, ƙwarai kuwa, maganar haka take kuma n gamsu sosai. Kawai bayan na gama Ci akwai wani abu ɗaya da na gane.
Ta ce, me ka gane?
Ya ce, Ƙwai ɗaya baya isa har sai mutum ya Ci guda huɗu...!!