Da zarar an sanya auren yarinya, sai iyayenta (Mata) suyi ta banka mata jiƙe-jiƙe babu gaira

Da zarar an sanya auren yarinya, sai iyayenta (Mata) suyi ta banka mata jiƙe-jiƙe babu gaira babu dalili, maimakon su mai da hankali wurin nuna mata abin da yake cikin rayuwar aure wanda zai dawwamar da zaman lafiya tsakanin ta da mijin.

Yarinya ta je tayi da wahalar da ɗan mutane, kwana biyu in bata samu yadda take so ba, kamar yadda aka ɗora ta akan wancan jiƙe-jiƙe sai ka ji ana hide my ID, ai ta faman zagin mijin (innocent soul).

Dan Allah iyaye ku daina wannan abun, ku ilmantar da 'ya 'yan ku yadda zasu tsaftace jikkunansu yafi alheri sau dubu akan wancan jiƙe-jiƙen da kuke ɗirka musu. 

Kun san dai maza da son tsafta, da tsafta kaɗai sai 'yar ku ta zauna lafiya da mijinta ko babu jiƙe-jiƙe.

Post a Comment

Previous Post Next Post